News
An kubutar da mahajjata aikin hajjin bana
Daga Yasir sani Abdullahi
An kubutar da mahajjata aikin hajji a jahar sokoto da Yan bindiga suka KAIWA hair
Bbc Hausa ta rawaito Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da kai hari kan jerin motocin maniyyata aikin Hajji da suka fito daga karamar hukumar Isa.
Maniyyatan suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Sokoto, babban birnin jihar domin tashi zuwa kasar Saudiyya, a lokacin wasu da ake zargin barayin daji ne suka auka wa ayarin motocinsu.
Sai dai sanarwar da gwamnatin Sokoton ta fitar ta ce maniyyatan sun isa garin Sokoto lafiya tare da rakiyar jami’an tsaro.
A cewar Kamishinan Sadarwa, Isah Bajini Galadanchi, tuni an ci gaba da shirye-shiryen kwashe maniyyata aikin Hajjin zuwa kasa mai tsalki ba tare da wata matsala ba.
Dama yankin Isa da ke Gabashin Sokoton na daga cikin wuraren da yan fashin daji ke kai hare-hare sosai a Arewacin Najeriya.
A nan ne watannin da suka gabata ake zargin yan fashin dajin sun kone motar fasinja dauke da mata da kananan yara, yayin da suke kokarin ficewa daga yankin don tsere wa rikici.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
