Sports
Phillips zai isa City yau, Barca za ta mika £60m don dauko Raphinha
Daga kabiru basiru fulatan
Barcelona ta shirya mika tayin da Leeds United ke bukata na fam miliyan 60 kan dan wasan gabanta Raphinha, a kokarinta na shiga gaban Chelsea a cinikin.
2023: Gwamnati Za Ta Tabbatar An Yi Sahihin Zaɓe -Buhari
Sai dai Chelsea na ci gaba da tattaunawa da Juventus don kokarin daukar mai tsaron bayanta Matthijs de Ligt, duk da bukatar kungiyar ta Turin ita ce a biya kudin warware cinikinsa fam miliyan 102.
Kazalika kungiyar Stamford Bridge din har yanzu tana da sha‘awar daukar mai tsaron bayan Faransa da PSG Presnel Kimpembe.
Manchester City ta ce ba za ta sayar da Nathan Ake ba, matsawar ba ta samu wanda zai maye madadinsa ba.
A Italiya Juventus na son saye dan wasan gaban Liverpool da Brazil Roberto Firmino, a wani yarjejeniyar musaya da Adrien Rabiot.
West Ham kuwa ta kara kaimi don ganin ta dauko dan wasan Ingila da Manchester United, Jesse Lingard kyauta, duk da tana sony a rage yawan albashinsa.
Wolves ta samu shawo kan dan wasan takiyarta Ruben Neves ya cigaba da zama Molineux, bayan da ta aminta ta biya fam miliyan 75 da aka saka masa.
Shi kuwa dan wasan tsakiyar Leeds United Kalvin Phillips, zai yi gwajin lafiya a Manchester City, bayan kungiyarsa ta aminta da tayin fam miliyan 45 kansa.
A nan kuma Manchester United ce tasa zare da Newcastle, wurin kokarin sayen mai tsaron bayan Monaco a Faransa Benoit Badiashile.
Karo na uku kenan Bayern Munich na watsi da tayin Barcelona kan dan wasan gabanta Robert Lewandowski. Munich na son fam miliyan 43 ne kansa.
