Connect with us

Sports

Manchester United: Cristiano Ronaldo na son barin ƙungiyar

Published

on

Ronaldo

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ɗan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo na son ƙungiyar ta ƙyale shi ya koma wata daban idan ta samu tayin da ya dace a kansa kafin fara sabuwar kaka a bana.

 

Advertisement

Yunwa ta kashe yara biyu a Sudan ta Kudu

Ɗan wasan na Portugal mai shekara 37 ya koma filin wasa na Old Trafford da taka leda daga Juventus a ƙarshen kakar bara.

Advertisement

Sai dai duk da cewa shi ne wanda ya fi ci wa United ƙwallaye – kuma na uku a gasar Premier baki ɗaya – ana ganin ƙungiyar ba ta taka rawar gani ba a kakar da aka kammala.

An fahimci cewa United ba ta da niyyar sayar da Ronaldo a yanzu.

Advertisement

Duk da cewa ƙungiyar ba za ta so rabuwa da ɗaya daga cikin ‘yan wasa mafiya ƙwarewa ba a duniya, sai dai tafiyarsa ka iya taimaka wa sabon koci Erik ten Hag gano maganin wasu matsaloli.

Ronaldo da Harry Maguire sun gwabza game da wanda za a bai wa kyaftin ɗin ƙungiyar a kakar da gama, yayin da tsarin ƙwallon kai hari da mai horarwa na riƙo Ralf Rangnick ya so ya aiwatar ya gamu da cikas saboda Ronaldo ya ƙi ya saba da tsarin.

Advertisement

United ta ƙare kakar a mataki na shida a Premier League, abin da ke nufin ba za ta buga gasar Zakarun Turai ba ta Champion League, sai dai Europa League. Sai dai ɗan wasan ya fi son buga Champions League.

Ɗan wasan da ya lashe kambin gwarzon ɗan ƙwallon duniya sau biyar na da shekara ɗaya da ta rage a kwantiraginsa da kuma zaɓin tsawaita shi na shekara ɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending