Sports
Ronaldo ya roki United ta sallame shi zai yi gaba
Daga kabiru basiru fulatan
Cristiano Ronaldo ya bukaci kungiyar da yake dokawa wasa yanzu haka Manchester United da ya yi wa Allah ta barshi ya yi gaba, muddun har ta samu tayin da ya dace da shi.
An cire mukaddashin Babban Akantan Najeriya
Dan wasan gaban na Portugal, mai shekaru 37, ya koma Old Trafford daga Juventus a bazarar da ta wuce.
Duk da cewa Ronaldo, shine dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a kakar wasan da ta wuce – kuma na uku a gasar Premier – ana kallon kakar wasannin da ta shude a matsayin babbar koma baya a gareshi.
United ta kare a matsayi na shida a teburin Premier don haka ta rasa tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai.
Hakan na nufin Ronaldo, wanda ke da sauran kwantiragin shekara daya da United, zai fuskanci doka wasannin gasar Europa a karon farko.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
