Entertainment
Daraktan Shirin Izzar So Ya Rasu
Daga Khadija Abdullahi Mahmud
Allah Ya yi wa daraktan shirin Izzar So mai dogon zango, Nura Mutapha Waye rasuwa.
Yau ake gudanar da taron ECOWAS a Ghana
Lawan Ahmad ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihirrajiuna. Allah Ya karbi rayuwar Nura Mutapha Waye, daraktan fim din Izzar So.”
Marigayin ya dade ana damawa da shi a Masana’antar Kannywood, amma fim din Izzar So din ya daga tauraronsa.
Za a yi jana’izarsa ne da misalin karfe 11 na safiyar nan a gidansa da ke unguwar Goron Dutse a Kano.
Advertisements
