Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya za ta ɗauki mutum miliyan ɗaya aikin ƙidaya

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Hukumar kidaya ta Najeriya NPC ta ce gwamnati za ta ɗauki ƴan ƙasar miliyan daya aiki domin gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2023.

Hukumar ta ba da tabbacin cewa, an samar da kyakkyawan tsarin gudanar da ƙidayar don hana ƴan siyasa da masu mummunar aniya amfani da wannan dama.

Ministan Ilmi Ya Buƙaci Adalci Wajen Ɗaukar Ɗaliban Makarantun Unity

Jaridar Daily Trust ta rawaito kwamishinan hukumar mai kula da jihar Ekiti Mista Deji Ajayi na bayyana hakan a Ado Ekiti, jiya, a wani taron manema labarai da ya kira kan kidayar gwaji da za a gudanar a jihar.

A yayin da yake bayyana mahimmancin kidayar jama’a ga gina kasa, Ajayi ya ce kungiyoyi masu zaman kansu za su yi amfani da kididdigar yawan jama’a wajen tsara yadda za a dauki matasan Najeriya aiki ta hanyar sanin adadin yawan jama’a.

Advertisement

“Gwamnati za ta kuma yi amfani da irin wannan kididdiga don tsara yadda za a taimaka wa matasanmu, da dalibanmu da kuma biyan bukatun lsauran jama’ar ƙasa’ in ji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending