News
Za a ba wa kamfanonin layukan sadarwa a Najeriya wa’adin kwana 30 don shawo kan matsalolin kwastomoninsu
Daga Khadija Abdullahi Mahmud
Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta shirya ba wa kamfanonin sadarwa a kasar wa’adin kwanaki 30 don shawo kan duk wasu matsaloli da masu amfani da layuka da sauran hanyoyin sadarwa ke fama da su.
A cewar hukumar, idan mai amfani da layi ya mika ƙorafinsa amma aka ƙi a saurare shi, zai iya sanar da ita bayan kwanaki 30, inda ita kuma za ta dauki matakin da ya dace.
Gwamnatin Najeriya za ta ɗauki mutum miliyan ɗaya aikin ƙidaya
An dai bayyana hakan ne cikin wani sabon daftarin dokokin ayyuka na hukumar da aka ɗora a shafinta na Internet.
Masu amfani da wayoyin hannu a Najeriya dai sun jima suna ƙorafi kan yadda kamfanonin layuka a ƙasar ke nuna halin ko in kula da ƙorafe-ƙorafensu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
