News
Jirgin ruwa ya kife da mutane 20 a Legas
Daga yasir sani Abdullah
Akalla mutum biyu ne suka mutu, bayan kifewar wani jirgin ruwa a Legas.
An ceto mutum 15 daga 20 da ke cikin jirgin, yayin faruwar lamarin a yankin Victoria Island.
Shafin Twitter ya maka gwamnatin Indiya a gaban kotu
A wata sanarwa da shugaban hukumar kula da sufurin ruwa ta jihar Oluwadamilola Emmanuel, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu ba a kai ga gano fasinjoji uku ba.
Emmanuel ya ce bayan faruwar lamarin jami’an hukumarsa sun garzaya wajen da lamarin ya faru domin kubutar da mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar haɗarin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
