News
Rikicin PDP: A shirye nake in sasanta da Wike – Atiku
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
A yau Alhamis ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyar sulhu da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Atiku ya ce a shirye yake ya sasanta da Wike domin maslahar jam’iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai a
Osogbo, babban birnin jihar Osun, Atiku ya dage cewa babu wani bangare a cikin PDP.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya dage cewa PDP ta hade wuri Vida.
“Wasan kwaikwayo ne na dandalin sada zumunta. Babu wani abu kamar bangaren Wike ko wani bangaren Atiku. Dukka Iyalan PDP daya ne.”

Akan shirin ganawa da Wike domin yin sulhu, kuma Atiku ya ce: “Me zai hana? Ina kofata abude take da hakan.”
“Wasu mutane kan yi fushi idan abubuwa ba su tafi yadda suke ba da sauransu. Za mu shawo kan hakan. Ina da dukkan imani cewa za mu yi hakan,” ya kara da cewa.
Wike dai bai ji dadin zaben da Atiku ya yi wa Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takarar sa.
Atiku ya yi watsi da shawarwarin kwamitin da ya kafa domin zabar abokin takararsa, bayan nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP.
Kwamitin mai mutum 16 ya ba da shawarar Wike, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na jam’iyyar, amma Atiku ya zabi Okowa.
A wani labarin kuma na daban.
Yan bindiga sun kai hari kan jami’an INEC a Enugu
Akalla mutane biyu ne aka kwantar a asibiti bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.
Shugaban Hukumar INEC, a sashen Watsa Labarai da Ilimantar da masu Zabe, Festus Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Alhamis.
Ya ce maharan sun lalata na’urar tantance masu kada kuri’a guda biyu a yayin harin
Sanarwar ta bayyana cewa an kai wa jami’an hari ne a yayin da suke ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a (CVR) a wata makarantar firamare da ke Umuopu da ke Umuozzi Ward 19 a jihar Enugu.
Ya ce, “’yan bindigar sun yi ta harbe-harbe ba kakkautawa don tarwatsa masu rajista da jami’an rajista. A rikicin da ya biyo baya, daya daga cikin ma’aikatanmu ya samu raunuka kuma yana karbar magani a asibiti,” in ji sanarwar.
“An yi asarar injunan rajistar masu kada kuri’a guda biyu da kayayyakin ma’aikata kamar wayoyin hannu.
“Saboda haka, an dakatar da rajistar masu kada kuri’a a gundumar a Igboeze North.”
A cewar Okoye, hukumar ta kai rahoton lamarin ga hukumomin ‘yan sanda a jihar Enugu domin fara bincike
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
