Connect with us

News

An kama Wani fursuna da ya tsere a kurkukun kuje

Published

on

Daga yasir sani Abdullahi

Rundunar Yan SANDAN jahar katsina da ke arewacin Nigeria ta ce Jami,anta sunyi nasarar kama Wani fursuna Daya da ya tsere daga kurkukun kuje da ke Abuja babban birnin tarayya kasar

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ya fitar

A jiya juma,a’ ya ce an kama fursunan ne mai suna Kamala Abubakar a wani samame da aka kai a maboyar bata-gari a jihar.

‘Yan bindiga sun kai hari kan gidan-yarin na Kuje ne a ranar 5 ga watan Yuli , inda aka tabbatar da cewa fursunoni 879 ne suka tsere, cikin su kuwa har da wadan da ake zargi Yan Boko Haram ne

Sai dai fursunoni da dama sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman fursunoni 443.

Advertisement

Tun bayan faruwar lamarin, an yi nasarar sake kamo kadan daga cikin fursunonin a wasu sassan kasar, da suka hada da jihar Ogun da Nasarawa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending