Connect with us

News

Zaɓen Osun: Jami’an EFCC sun fito kan tituna

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Jami’an hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC sun fito kan tituna a Jihar Osun

Wakilan BBC da ke jihar sun ce sun hange su a Ikirun da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun a jihar.

Ko a jiya Juma’a sai dai ƴan sandan Najeriya suka bayyana cewa suna aiki tare da EFCC domin daƙile batun sayen ƙuri’a a zaɓen jihar.

  1. Jami’an INEC na shirya rumfunan zaɓe domin soma jefa ƙuri’a

    ,,

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben Jihar Osun.

    Wakilan BBC da ke jihar sun bayyana cewa tun ƙarfe 7:00 na safe wasu jami’an na INEC suka soma hallara rumfunan zabe.

    A ƙa’idance za a soma tantancewa da kuma jefa ƙuri’a 8:30 na safe a kammala 2:30 na rana.

    Advertisement
    .
    .
  2. ..

    A yau jama’ar Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya za su gudanar da zaɓen gwamna a jihar.

    Ƴan takara 15 ne ake sa ran za su fafata a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar.

    Ƴan takarar sun haɗa da;

    • AP: Akinade Akanmu Ogunbiyi
    • AAC: Awojide Peter Segun
    • ADP: Kehinde Munirudeen Olumuyiwa A Atanda
    • APC: Adegboyega Isiaka Oyetola
    • APM: Awoyemi Oluwatayo Lukuman
    • APP: Adebayo Adeolu Elisha
    • BP: Adeleke Adesoji Masilo Aderemi Adedapo
    • LP: Yussuff Sulaimon Lasun
    • NNPP: Rasaq Oyelami Saliu
    • NRM: Abede Adetona Samuel
    • PDP: Adeleke Ademola Jackson Nurudeen
    • PRP: Ayowole Olubusuyi Adedeji
    • SDP: Omigbodun Oyegoke Akinrinola
    • YPP: Ademola Bayonle Adeseye
    • ZLP: Adesuyi John Olufemi

    An kirkiri jihar Osun karkashin mulkin soji na Ibrahim Babangida, daga tsohuwar jihar Oyo a ranar 27 ga watan Agustan 1991.

    Isiaka Adeleke, dan uwa ga dan takarar jam’iyyar PDP ne ya fara zama gwamnan jihar a watan Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993, lokacin da gwamnatin mulkin soji karkashin Ibrahim Babangida ta rusa mukaman siyasa bayan soke zaben June 12

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending