News
Dalilin da ya sa APC ta sha kashi a zaben gwamnan jihar Osun
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Tsohon mai bai wa gwamnan Osun shawara kan ƙabilu mazauna jihar, Muhammad Bashir, ya bayyana dalilai na siyasa da suka sa jam’iyyar APC mai mulki ta fadi a zaɓen gwamnan jihar.
A wata hira da BBC Alh. Bashir wanda limami ne kuma jami’i a gwamnatin tsohon Gwamna Rauf Aregbesola, ya ce rikicin cikin gida ne ya kayar da jam’iyyar tasu.
Ya ƙara da cewa kusan kashi 90 cikin 100 na mutanensu PDP suka zaɓa, saboda gwamnatin Gboyega Oyetola “ta yi watsi da su”.
ya ci gaba da cewa “Makomarmu yanzu ita ce mu shiga taitayinmu, yanzu abin da muka faɗa wa shugabanni suka ƙi ji yanzu za a koma a sake shiri,” in ji shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
