Connect with us

News

NDLEA ta kama wata mata za ta yi safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Oman

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta kama wata mai suna Opoola Mujidat, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi zuwa Oman, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.

Advertisement

Dalilin da ya sa APC ta sha kashi a zaben gwamnan jihar Osun

An kama ta ne bayan hukumar ta kama wasu fasinjoji biyu da ke tafiya Oman a ranar Litinin, 11 ga Yuli.

 

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce an kama fasinjojin biyu, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi kafin su hau jirgi.

 

“Fasinjojin, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi, suna tafiya tare zuwa kasar Oman dake Gabas ta Tsakiya a cikin jirgin kasar Habasha a ranar Litinin 11 ga watan Yulin shekarar na ta 2022 inda jami’an NDLEA suka tare su a filin jirgin.

Advertisement

 

“A binciken da aka yi a cikin jakunkunan su, an gano kullin tabar wiwi da aka boye a cikin wata jaka dauke da kayan abinci, wanda Kazeem ke dauke da ita.”

 

“Nan da nan Kazeem da Omoniyi suka sanar da jami’an yaki da miyagun kwayoyi cewa Mujidat da ke kusa da wurin ce ta ba su jakar da ke dauke da haramtattun kayan a filin jirgin, nan take kuma aka kama ta.”

 

A cewar sanarwar, Mujidat ta yi ikirari cewa ta kawo kayan ne da nufin fasinjojin biyu su bawa mijinta dake can a kasar Oman din.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending