News
Za mu yi maganin manyan jami’anmu da ke haɗa kai da ɓarayi’
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce a shekara mai zuwa ta 2022, zai ta matsa ƙaimi tare da sa ido matuƙa kan manyan jami’anta waɗanda ke haɗa baki da masu satar ɗanyen mai da kuma masu aikata laifuka a cikin teku.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hafsan sojin ruwan ƙasar, Vice Admiral A.Z Gambo wanda ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama da laifin haɗa kai da masu aikata laifuka domin yin maƙarƙashiya ga tsarukan da rundunar sojin ruwa ta saka lallai za su gamu da fushin rundunar inda za a hukunta su daidai da yadda doka ta tanada.
Mista Gambo ya bayyana haka ne a lokacin da ake ƙarin girma ga wasu manyan jami’an rundunar.
Ya bayyana cewa rundunar na iya bakin ƙoƙarinta wajen kare tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar yaƙar masu satar ɗanyen man fetur da masu aika wasu laifukan.