Connect with us

Opinion

Garuruwa uku da aka fi sace mutane a kan titin Kaduna-Abuja

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Zahraddin

Matsalar garkuwa da mutane na ci gaba da tayar da hankulan jama’a a arewacin Najeriya. Lamarin ya fi ta’azzara a jihohin arewa maso yamma irin su Zamfara da Katsina da Kaduna.

Sai dai hankulan jama’a na ƙara karkata kan titin Kaduna zuwa Abuja sakamakon sace mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba da kuma kashe wani tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

Advertisement

A baya ana ta murna cewa an samu saukin matsalar garkuwa da mutane a wannan shahararriyar hanya.

Hukumomin Najeriya sun ɗauki matakan kariya tare masu yawa da suka hada da girke sojoji masu yawa ciki har da wasu sojoji mata da suke sintiri a kan titin.

Masana harkokin tsaron sun ce wadannan matakai sun yi matukar tasiri a zahiri, amma kuma abin da ya faru a karshe makon jiya ƙara tayar da hankulan al’ummar kasar.

Advertisement

Bayanai sun nuna cewa akwai garuruwa uku da masu garkuwa da mutane suka fi cin karensu babu babbaka a wannan yanki – garuruwan su ne Jere da Katari da kuma Rijana.

Malam Kabiru Adamu shi ne shugaban kamfanin Becon Consultancy da ke nazari kan harkokin tsaro a Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa akwai dalilai guda uku da suka sanya masu garkuwa da mutane suke yawan tare mutane a wadannan garuruwa.

“Babu wasu kwararan bincike da aka gudanar a ƙasa, amma abin da ya bayyana a zahiri shi ne wadannan ƙauyuka na da dazuka da tsaunuka ga kuma ruwa a gefensu,” in ji shi.

Advertisement

Bari mu duba kowanne daga cikinsu:

Katari

Garin Katari yana da nisan kilomita 61 daga Kaduna kuma yana daya daga cikin garuruwa masu matukar haɗari da masu garkuwa da mutane ke sace mutane.

Malam Kabiru Adamu ya ce garin Katari na da fadin daji da kuma fadin ƙasa ga kuma nisa idan ana tafiya musamman ga wadanda ba su san kanshi ba.

Advertisement

Ya ce duk da cewa ba su da takamaiman bincike kan abin da ya sanya wannan gari ya zama matattarar masu garkuwa da mutanen amma tsaunukan da ake da su suna cikin abubuwan da ke ba su damar gudanar da muggan ayyukansu.

Baya ga fadin daji da kuma tsaunuka da wannan gari ke da shi, yana kuma da rafuka wadanda rashin sanin nisansu yake ƙara jefa jami’ain tsaro cikin haɗari mai yawa.

A wannan ƙauyen an kama mutane da dama an kuma kashe wasu da ba za a iya fadin adadinsu ba. Amma cikin fitattun mutanen da aka kama a ƙauyen akwai tsohon shugaban Hukumar Ilimin Bai-daya ta kasa wato UBEC, Dr. Mohammed Mahmood tare da ‘yarsa Yasmin a 2019.

Advertisement

Kafin nan, a tsakanin wannan gari ne zuwa Jere aka kashe wasu mutum hudu a ranar 22 ga watan Yuli 2018 ciki har da tsohuwar Kwamishinar Ilimi ta jihar Katsina Farfesa Halimatu Idris, kamar yadda ‘yarta ta tabbatarwa da BBC a lokacin.

A wannan gari ne aka sace Sarkin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru na jihar Zamfara wanda ya kwashe sama da wata guda ba a ji duriyarsa ba. Rahotanni sun ce bibiyarsa aka rika yi har sai da ya zo wannan yanki mai hadari tukunnan aka kama shi.

Abu na baya-bayan nan da ya faru shi ne kashe tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara da aka yi a wannan hanya a kusa da wannan gari, Alhaji Sagir Hamidu.

Advertisement

Jere

Garin Jere mai nisan kilomita 105 na yankin karamar hukumar Kagarko a Kudancin Kaduna, kamar dai Katari yake a wajen haɗari.

Mafi yawan hare-haren da ake kai wa Katari suna da alaƙa da Jere saboda suna kusa da juna.

An dade ana kai wa mutane hare-hare da ke wannan ƙauyen, domin kuwa ko a 2014 sai da aka kai wa Sarkin Jere, Dr Sa’ad Usman hari a kusa da garin inda ya samu raunuka masu yawa.

Advertisement

Sai dai Alhaji Bashir Isa Danmajen Jere ya ce wannan hari na da alaka da wata rashin jituwa da ta faru tsakanin sarkin da wasu mutane.

Ko a watan Mayun 2021, sai da wadannan mutanen suka tare hanya suka riƙa kama matafiya a kan hanyar ta kusa da garin Jere da misalin karfe 4 na yamma.

Tsohon Sanatan Kaduna Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ya samu kira daga wasu matafiya suna ba shi labarin an tare su a garin.

Advertisement

A Najeriya an taɓa kai matukar da labarin sace mutane ya koma ba wani labari ba, saboda yawan yadda ake tsare mutane ake garkuwa da su.

Shi ma wannan gari in ji Malam Kabiru yana da matukar daji mai fadi ga surƙuƙi da yake da shi, akwai tafki-tafki a karamar hukumar Kagarko da Jere ke ciki.

Rijana

Rijna shi ne gari na uku mai hadari wanda ke da nisan kilo mita 59.4 daga Kaduna. Wuri ne da aka girke sojoji da ‘yan sanda amma hakan bai hana masu garkuwa da mutane gudanar da ayyukansu ba.

Advertisement

Gari ne da ake yi masa hangen dala ba shiga birni ba, domin da yawa suna zuwa Rijana za su ji kamar sun shiga Kaduna daga Abuja, amma idan daga Kaduna ne zuwa Abuja to ana kallonsa a mafarin tafiya.

A cikinsa an kama jama’a da yawa, an kashe wasu da dama, kamar Jere da Katari garin Rijana na da tsaunuka da suke zama mafaka suke gudanar da ayyukansu ba tare da tashin hankali ba.

Abin da ke ciwa jami’an tsaro tuwo a kwarya‘ 

Advertisement

Malam Kabiru Adamu ya ce daji guda ne ya hada Jihohin Kaduna da Neja da Zamfara, ta can bangaren kuma ya haɗa Jihar Kebbi da wadannan sauran jihohi.

Bayan maganar daji in ji Malam Kabiru, akwai matsalar kundin tsarin mulki da ya takaita wa jami’an tsaro shiga daji domin yaƙar wadannan bata-gari.

“A tsari, jami’an (Forest Guard) wadanda ke lura da dazuka ne kawai suke da hurumin shiga daji domin ba shi kariya, da kuma fatattakar bata garin da ke cikinsa.

Advertisement

“Babu wani jami’in tsaro da yake da hurumin shiga daji domin yakarsu, sai dai idan shugaban ƙasa ne ya amince a yi hakan a kansu.

“Ko an shiga za a yake su hakan na da iyaka saboda ba ‘yan ta’adda ba ne, ba za a yake su ba kamar ‘yan Boko Haram,” in ji Kabiru Adamu.

Muhimmancin hanyar Kaduna-Abuja

Advertisement

Masana al’amuran yau da kullum sun sha bayyana muhimmancin wannan hanya ga yankin arewacin Najeriya.

Tana da matukar muhimmanci ta bangaren kasuwanci saboda sai an bi ta kanta ne ake isa cibiyar kasuwancin arewa wato jihar Kano.

Kaduna in ji masanan ita ce tamkar cibiyar gudanarwar arewacin Najeriya, domin a nan ne ake gudanar da tarukan da suka shafi arewacin kasar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *