Connect with us

Opinion

Ƙungiyoyi sun buƙaci Ganduje ya sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil ya koma na Bashir Tofa

Published

on

Spread the love

Ƙungiyoyi sun buƙaci Ganduje ya sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil ya koma na Bashir Tofa

Gamaiyar Ƙungiyoyin Farar Hula a Jihar Kano sun buƙaci Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya karrama marigayi Bashir Othman Tofa ta hanyar sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha dake Wudil, KUST zuwa sunan marigayin.

Wannan kira na ƙunshe ne a wata sanarwa da Shugaban Gamaiyar Ƙungiyoyin, Kwamaret Ibrahim Wayya ya sanyawa hannu kuma a ka rabawa manema labarai a Kano a jiya Talata.

Advertisement

Sanarwa ta ce Tofa ya chanchanci Gwamnatin Jihar Kano ta yi masa wannan karramawar idan a ka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar ta fuskar siyasa, tattalin arziki, Ilimi da dai sauransu a jihar ta Kano da kasa baki ɗaya.

A cikin saƙon su na ta’aziyya ga Iyalai da al’ummar Jihar Kano, Gamaiyar Ƙungiyoyin ta yi fatan Ganduje zai yi duba don karrama gwarzo ɗan kishin ƙasa wanda Kano ba za ta taɓa mantawa da gudummawar sa ba.

Sun yi fatan “Allah Ya gafarta ma sa Ya sa aljanna ta zamo makomarsa, ya kuma baiwa iyalansa da al’ummar Jihar Kano jakurin juri wannan gagarumin Rashi da zai yi wuya a samu Wanda Zai cike gibin da ya bari.”

Advertisement

Alhaji Bashir Othman Tofa ya rasu ranar Litinin ɗin da ta gabata ya na da shekaru 74 bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *