Connect with us

Opinion

Ayyukan da wasu ƴan Najeriya ke buƙata a 2022

Published

on

DE36CDF0 6BD4 42BF BED5 66EF7F71F540 cx0 cy2 cw0 w408 r1 s
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

A kowace shekara, mutane da dama a faɗin duniya suna da buri daban-daban da suke so su ga sun cimma, haka kuma suna da fatan da suke da shi musamman ga ƙasashensu.

Akasari jama’a na fatan samun ci gaba daban-daban da suka shafi siyasa ko tattalin arziki ko mulki ko harkar lafiya ko noma da dai sauransu.

Kwanaki kaɗan bayan shiga sabuwar shekara, BBC ta tambayi mabiyanta a shafukan sada zumunta irin ayyukan ci gaban ƙasa da suke so gwamnatocinsu su yi musu.

Advertisement

Ɗumbin jama’a sun ta bayyanara’ayoyi daban-daban kan irin abubuwan da suke buƙata.

Zaman lafiya da tsaro

Babban abin da jama’a suka yi ta magana a kai shi ne batun tsaro inda suka yi ta kira ga gwamnati ta tabbatar ta samar da tsaro a wannan sabuwar shekara.

Mutane da dama ciki har da Sanusi Shehu Gaya na buƙatar samun zaman lafiya a Najeriya.

Advertisement

Bisa wannan buƙata ta jama’a da dama BBC ta tuntuɓi Barrista Bulama Bukarti kan irin abubuwan da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai a 2022 dangane da batun tsaro.

A cewarsa, maganar tsaro ne mafi girman al’amari a duniya ba sai ma Najeriya ba.

“Idan babu tsaro, babu abin da yake yiwuwa a ƙasa, maganar tattalin arziki, maganar ilimi, maganar zamantakewa, babu abin da zai yiwu matuƙar babu tsaro,” in ji Barrista Bukarti.

Advertisement

Barrista Bukarti ya bayyana cewa zaɓen 2023 da ƴan Najeriya ke fatan gani, idan ba a dauki kwararan matakai ba, zai yi mummunar illa ga zaɓen.

“Abu na farko da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta sauya tsarinta na yaƙi da ta’addanci, abin da gwamnati take yi a yanzu shi ne sojoji sun zama ƴan kariya, jira suke sai an kawo hari su kai ɗauki,” kamar yadda Barrista Bukarti ya yi zargi.

Inganta tattalin arziki

Inganta tattalin arziki da samar da ayyukan yi da samun sauƙin rayuwa na daga cikin abubuwan da jama’a suka ce suna buƙata.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *