Connect with us

News

Ƴan Ƙungiyar Dattijan Arewa sun fashe da kuka yayin ta’aziyyar Bashir Tofa a Kano

Published

on

FB IMG 16409937713379550
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Wasu fitattun ƴan siyasa, abokai da abokan gwagwarmaya, a ƙarƙashin inuwar Muryar Dattijan Arewa, NEF, sun ziyarci Jihar Kano a yau Laraba domin ta’aziyyar Bashir Othman Tofa, wanda ya rasu a ranar Litinin.

Shi dai marigayi Tofa na cikin waɗanda su ka kafa Muryar Dattijan Arewa.

Advertisement

Tawogar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban NEF, Farfesa Ango Abdullahi, ta isa gidan Marigayin da misalin ƙarfe 1:15 na rana.

Isar su ke da wuya, bayan da ya tashi ya na gabatar da ƴan ƙungiyar da kuma makasudin zuwan su ga iyalin marigayi Tofa, Nastura Ashraf, ɗan ƙungiyar kuma Shugaban Gamaiyar Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu na Arewa, sai ya fashe da kuka, inda daƙyar ma ya ƙarasa jawabin na sa.

Bayan nan kuma sai wani ɗan ƙungiyar, Mustapha B. Wali, da a ka umarce shi da ya yiwa mamacin addu’a, shima sai ya fashe da kuka.

Advertisement

Kafin ya fara kukan, Wali ya ce sun yi rayuwa tare da Marigayin tsawon shekaru 60, inda ya ce tare ma su ka yi karatu a birnin Landan.

Da ga nan sai ya fara addu’a ga mamacin, kuma a nan ne ya tsinke da kuka har ya kammala addu’ar.

A jawabin sa ga iyalan marigayin, kakakin NEF, Hakeem Bana Ahmed, ya suffanta marigayi Tofa a matsayin mutumin kirki wanda ya mutu yana tsaka da taimakawa al’umma.

Advertisement

A cewa sa, banda bakin cikin rabuwa da masoyi, amma mutuwar Tofa ta yi kyau sabo da ya bar kyawawan aiyuka da har abada ba za a manta da su ba.

“Ina kira da iyalin sa da ma matasa masu tasowa da su yi koyi da Bashir Tofa. Ina kira ga ƴaƴan sa da jikokin sa da su ci gaba a kan aiyukan alheri da ya ke yi da taimakon al’umma,” in ji Ahmed.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tawogar ta kai ziyara ga Attajiri, Alhaji Aminu Dantata, Sarkin Kano da kuma Mataimakin Gwamnan Kano duk a yau Laraba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *