Connect with us

News

Jonathan ya gamu da sarkakiya a titin 2023, Jiga-jigan APC ba su gamsu da sauya-shekarsa ba

Published

on

FB IMG 16418100825912811
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

Duk da zawarcin da wasu gwamnonin Arewa da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki suke yi, da wahala shigowar Dr. Goodluck Jonathan ta tabbata.

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Junairu, 2022 ya nuna cewa jagororin jam’iyyar APC ba su yarda da wannan shiri ba.

Ana kishin-kishin cewa a halin yanzu gwamnonin kudu maso kudu ba su tare da Jonathan, kuma yunkurin tsaida ‘dan takararsa a Bayelsa ya ci tura.

Advertisement

Rahoton ya tabbatar da cewa kan tsohon shugaban na Najeriya ya rabu kan sake neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 ko ya hakura ya zama dattijo.

Zama a PDP ya yi zafi Wani gwamna a yankin Neja-Delta da Jonathan ya fito yana cikin manyan masu adawa da shi, ya sha alwashin ba za a ba shi damar tsayawa takara a PDP ba.

Wani bincike da jaridar kasar tayi, ya nuna sabanin da ake samu ne ya jawo gwamnonin Arewacin Najeriya akalla uku fuk su na zarwacin Jonathan.

Advertisement

Za ta sabu kuwa – ‘Yan APC Ko da wadannan gwamnoni na APC da suka fito daga Arewa sun dage a kan bakarsu, mafi yawan gwamnonin jam’iyyar sam ba su gamsu da wannan shirin ba.

Masu adawa da shigowar tsohon shugaban kasar cikin jam’iyyar APC su na ganin cewa yin hakan ya na nufin babu dalilin hambarar da PDP a zaben 2015.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa Buhari bai da ‘dan takarar da yake goyon baya a zaben shugaban kasa, amma bai bada goyon bayan a jawo wanda ya gada ba.

Advertisement

Haka zalika jiga-jigan APC da-dama ba su farin ciki da rade-radin shigowar Jonathan cikin jam’iyyar su, suna ganin bai da wani nauyi idan an je filin zabe. Nairaland yace Goodluck Jonathan yana da wasu tsofaffin shugaban kasa akalla biyu da ke tare da shi.

Mulki zai bar Arewa?

Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Nwabueze Ngige yana ganin ya kamata mulki ya bar Arewacin Najeriya, ya koma hannun ‘Dan yankin kudu a 2023.

Advertisement

Tsohon gwamnan na jihar Anambra yace an yarda da tsarin karba-karba a lokacin da aka kafa jam’iyyar APC, sai dai ba a yi wannan alkawarin a rubuce ba.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *