Connect with us

News

Najeriya ta bayar da tallafi ga waɗanda gobarar kasuwar Nguru ta shafa

Published

on

Spread the love

Daga Usman Abdullahi jibirin Ngurun Yobe

Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta bayar da tallafin abinci da kayayyaki ga waɗanda gobarar da ta tashi a kasuwar Nguru da ke Jihar Yobe ta shafa.

A makon da ya gabata ne sama da shaguna 300 suka ƙone a kasuwar.

Advertisement

Kafar watsa labarai ta Channels a Najeriya ta ruwaito cewa Ministar Ma’aikatar Jinkai da Cigaban Al’umma da Kare Afkuwar Bala’i wato Sadiya Umar-Faruk ce ta miƙa kayayyakin a ranar Alhamis.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan wanda shi ne sanata mai wakiltar arewacin Yobe ya bai wa waɗanda lamarin ya shafa tallafin miliyan 10.

An yi asarar kayayyaki na miliyoyin nairori a yayin gobarar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *