Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce ta kuɓutar da wani matashi da ake zargin wasu yan damfara sun yi yunƙurin yi wa yankan rago.
Lamarin ya faru ne a wani gida a ƙaramar hukumar Dambatta a Kano.
Kakakin rundunar ƴan sandan DSP Abdullahi Kiyawa ya shaida wa BBC cewa sun sami labarin faruwar lamarin ne bayan da matashin da aka fara yankawa makogoro ya kai musu ƙorafi.
Ya ce nan take suka garzaya da shi asibiti.
Matashin, mai shekara 23, ya bayyana wa BBC cewa a dandalin sada zumunta na Facebook suka haɗu da wanda ake zargi da yunƙurin halaka shi.
A makon da ya gabata ma an kama wani matashi da ya yi wa wata yarinya ‘yar makotansu yankan rago a karamar hukumar Tofa a Kano, bayan ya nemi kudin fansa daga wajen iyayenta.