News
NIGERIA ce kasa ta Daya a Afirka bangaren noma n Shinkafa – Inji Emefiele.
Daga Yasir sani Abdullah
Gwamnan babban bankin kasa (CBN) Godwin Emefiele, ya ce, Nigeria ce kasar da tafi kowace kasa noman Shinkafa a nahiyar Afirka.
Gwamnan na CBN ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da dalar Shinkafa wadda aka yi ittifaki ita ce mafi girma a Duniya a birnin tarayya Abuja da safiyar talata
Ya ce, yanzu Nigeria tana nome Shinkafa tan miliyan tara a duk shekara.
“Kafin zuwan wannan gwamnati a shekarar 2014 kasar nan tana da kamfanonin sussukar Shinkafa guda shida ne kacal amma ya zuwa karshen shekarar da ta gabata akwai kamfanonin sussukar Shinkafa sama da hamsin”
“Kuma a waccan lokacin ana shigo da Shinkafa daga kasar Thailand kawai zuwa kasar nan da ta kai tan miliyan daya da dubu dari uku banda wadda ake shigo da ita daga sauran kasashe”
“Cikin wannan wa’adi mun yi iya kokarinmu wajen bai wa manoma miliyan hudu da dubu dari hudu da tamanin da tara da dari bakwai da tamanin da shida a sassa daban-daban na kasar nan, tallafin noma” a cewar Emefiele.