News
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kwamishina a Bayelsa
Daga kabiru basiru fulatan
Wasu ‘ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da Kwamishinan Ciniki da Kasuwanci na Jihar Bayelsa, Mista Otokito Oparmiola.
An jiyo cewa wasu mutane ɗauke da muggan makamai ne su ka yi garkuwa da Otokito daga gidansa da ke Otuokpoti, Ƙaramar Hukumar Ogbia.
Majiyoyi sun ce ƴan bindigar sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 11 na daren Alhamis inda suka yi harbi da dama don tsoratar da mutane kafin su wuce gidan Otokito inda aka garzaya da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
