News
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da malami da wasu mutane 4 a Yobe
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rundunar Ƴanan Sandan Jihar Yobe a yau Laraba ta tabbatar da sace Babagana Kachalla, Mataimakin Shugaban makarantar Central Primary, Buni Yadi da wasu mutane hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Madiya da ke Ƙaramar Hukumar Gujba a jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.
Abdulkarim ya lissafa sauran wadanda aka sace da su ka haɗa da Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da Hajiya Gana.
Ya ce wani Mala Boyema ne ya kai rahoton lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 8:20 na safiyar ranar Talata, ga ofishin ‘yan sanda na yankin da misalin karfe 10:37 na safe.
Kakakin ya ce, Boyema ya yi sa’a ya tsallake rijiya da baya daga garkuwar da maharan, ɗauke da muggan makamai suka yi a lokacin da ya bi ta shingen da su ka sanya a hanyar Madiya.
Sai dai ya ce daga baya maharan sun sako Gana.