Connect with us

News

Jirgin yaƙin sojin saman Nijeriya, Super Tucano ya hallaka wani kwamandan ISWAP, Mallam Ari da mayaƙansa

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Jirgin yaƙin Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa, NAF, Super Tucano da ke karkashin Operation Hadin Kai ya hallaka kwamandojin ISWAP da dama da sauran ‘yan ta’adda a Kirta Wulgo.

Jaridar PRNigeria ta tattaro bayanai cewa, an kashe babban kwamandan ISWAP, Mallam Ari, wanda ke kula da Kirta Wulgo, da wasu sojojin hayar da su ka dauko da ga ƙasashen waje da ke haɗa abubuwan fashewa, IED, ga ‘yan ta’addar, a yayin farmakin da jiragen yaƙin suka kai musu.

Wani babban jami’in leken asiri na soji ya ce an ba da izinin kai hare-haren ne bayan bayanan sirri sun gano sama da ‘yan ta’adda 40 ne suka samu wajen zama a yankin Arewa maso Gabashin Kirta Wulgo, kusa da wurin da ake zargin ISWAP ɗin ta kafa tutar ta.

Advertisement

“An kuma ga wasu dauke da makamai a kusa da wani gini na ƙwarya-ƙwarya da ke kusa, wanda hakan wata alama ce da ke nuna cewa ginin an yi shi ne domin haɗa manyan hare-hare.

“Bayan harin da aka kai ta sama, an ga wasu daga cikin ‘yan ta’addan da suka tsira da ransu suna kokarin kashe gobarar da ta tashi yayin da wasu kuma suka tsere.

“Hakika, gine-ginen sun kone sosai kuma an lalata su a yankin.”

Advertisement

“An kashe mayakan ISWAP da dama a harin da aka kai ta sama ciki har da wani Malam Ari wanda aka bayyana sunansa da Fiya na Kirta Wulgo.”

Fiya lakabi ne na matsayi na biyu a tsarin tsarin muƙaman ‘yan ta’addan.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ta NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da cewa rundunar ta kai wasu hare-hare a wasu yankunan da ke kusa da Kirta Wulgo, amma ta yi shiru kan adadin wadanda suka mutu ko kuma su wanene.

Advertisement
  • Kwanan nan shugabannin ISWAP sun yi sauye-sauyen mukamai saboda asarar wasu manyan mambobinta da aka kashe musamman ta hanyar kai hare-hare ta sama da jiragen NAF suka yi.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *