Connect with us

News

Shaye-shaye: Mahaifiya ta kai ɗanta kotu a Kano

Published

on

Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Masu iya magana na cewa abinda ya koro ɓera ya faɗa wuta to ya fi wutar zafi.

Wannan karin maganar ta yi daidai da lamarin da ya faru a Jihar Kano, yayin da mahaifiya, duk irin so da ƙaunar da uwa ke yi wa ɗanta, amma sabo da wannan ya addabe ta, sai ta kai shi gaban alkali domin a hukunta shi.

Mahaifiyar, wacce a ka sakaya sunanta, ta maka ɗan cikin nata a kotun shari’ar Muslunci mai lamba 1 da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano a jiya Talata.

Advertisement

Cikin kuka, mahaifiyar ta shaidawa kotun cewa ɗan nata ya na ɗauko mata magana kuma ya na shaye-shaye matuƙa kuma ya ƙi yin sana’a.

Ta ƙara da cewa domin ta tserar da shi da ga yin shaye-shayen, komai na rayuwar sa ta ɗauke masa iya daidai gwargwado amma duk da haka ya ƙi ya nutsu.

“Wallahi ko takalmin da ne ya tsinke ni zan gyara masa ko na sai masa wani, amma ya ƙi ya dena shaye-shaye da dauko min magana.

Advertisement

“Ya sha cewa ya dena amma bayan kwana biyu sai ka ga ya dawo ruwa,” in ji ta.

Daga bisani ne ta ke riƙon kotu da ta aike da shi gidan yarin ko hakan zai sa ya kintsu.

Da Alƙalin kotun, Munzali Tanko Soron-Ɗinki ya karanto wa matashin laifukan sa, sai ya amsa da bakin sa, inda ya nemi kotu da ta yi masa afuwa, ya kuma yi alƙawarin ba zai sake aikata munanan aiyukan ba.

Advertisement

Daga nan ne sai alƙalin ya bada umarnin a yi wa matashin bulala 30 sannan ya aike da shi gidan yari tsawon mako 2.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *