Uncategorized
YANZU-YANZU: Babu Abdullahi Abbas da Ɗanzago a sunayen shugabannin jam’iya na jiha da APC ta rantsar
Daga Muhammad Muhammad zaharddini
Yayin da Jam’iyyar APC ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga Febrairu, Kwamitin Riƙo na Jam’iyar APC ya rantsar da shugabannin jam’iya na jihohi 34 da Birnin Taraiya a yau Alhamis a Abuja.
Sai dai kuma kwamitin bai rantsar da shugabannin jam’iyyar na Jihohin Kano da Sokoto ba.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matakin ƙin rantsar da shugabannin jam’iyar a Kano da Sokoto ba ya rasa nasaba da rikicin jam’iyyar a jihohi biyun.
A jihar Kano, jam’iyar APC ta rage gida biyu, inda ɓangaren Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas, shi kuma tsagin Sanata Ibrahim Shekarau ya zaɓi Ahmadu Haruna Zago, kowannen su a matsayin shugabannin jam’iyar.
Jerin sunayen shugabannin da kwamitin ya rantsar a yau sun haɗa da, Dakta Kingsley Ononogbu (Abia), Alhaji Ibrahim Bilal (Adamawa), Augustine Enefiok Ekanem (Akwa Ibom), Basil Ejike (Anambra), Alhaji Babayo Aliyu Misau (Bauchi), Dakta Dennis Otiotio (Bayelsa), Mista Augustine Agada (Benue), Honorable Ali Bukar Dalori (Borno), da kuma Mista Alphonsus Orgar Eba. (Cross River).
Sauran sun haɗa da Elder Omeni Sabotie(Delta), Stanley Okoro Emegha (Ebonyi), Kanal David Imuse Mai ritaya (Edo), Barista Omotosho Paul Ayodele (Ekiti), Chif Ogochukwu Agballah (Enugu), Mista Nitte K Amangal (Gombe), Dr Macdonald Ebere (Imo), Hon. Aminu Sani Gumel (Jigawa), Air Comadore Emmanuel Jekada (Rtd) (Kaduna), Alhaji Muhammed Sani (Katsina), Alhaji Abubakar Muhammed Kana (Kebbi) Honorable Abdullahi Bello (Kogi).
Sai kuma Prince Sunday Adeniran Fagbemi (Kwara), Hon. Cornelius Ojelabi (Lagos), Mista John D Mamman (Nasarawa), Hon. Haliru Zakari Jikantoro (Niger), Chif Yemi Sanusi (Ogun), Injiniya Ade Adetimehin (Ondo), Prince Adegboyega Famodun (Osun), Hon Isaac Omodewu (Oyo), Hon Rufus Bature (Plateau), Chif Emeka Bekee (Rivers). Hon Ibrahim Tukur El-Sudi (Taraba), Alhaji Muhammed A. Gadaka (Yobe), Alhaji Tukur Umar Danfulani (Zamfara) da Alhaji Abdulmalik Usman (ABuja).