News
China, Rasha sun gargadi Amurka a game da girke dakaru a kusa da su
Daga yasir sani abdullahi
Russia da China sun chachaki Amurka game da irin mummunar rawar da ta ke takawa a Turai da yankin Asia wanda hakan ke kara rura wutar rashin jituwa a tsakanin yankunan biyu.
Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar shugaba Vladmir Putin na Russia da takwaran sa na China Xi Jinping.
Putin da Xi dai sun yi tattaunawar ne yayin da ake gab da bude gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsale wato Olympics na Hunturu, yayin da dukkanin kasashen biyu ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga Amurkar.
A wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen biyu suka fitar, sun yi watsi da yadda Amurka ke ci gaba da aike wa NATO dakarunta sama da dubu dari don shirin ko ta kwana game da kudurin Russia na mamaye Ukraine.
A cewar Russia a yanzu babban abin da ta ke bukata shine samun tabbaci daga NATO kan cewa ba za ta karbi duk wata tawagar dakaru daga Amurka ba, wanda hakan shine kawai hanyar dawo da zaman lafiya a yankin.
Baya ga hakan, Rusha ta kuma ce tana bukatar NATO ta ja kunnen Amurka game da kafa sansanin soji a duk wata kasa dake mamba a tsohuwar tarayyar Soviet, yin hakan a cewarta takalar fada ne kuma babu makawa zata mayar da zazzafan martani.
