Wata doka da ke buƙatar akasarin baligai a Austria su yi riga-kafin korona ta fara aiki.
Wannan doka wadda ita ce irinta ta farko a Tarayyar Turai na buƙatar duk wanda ya kai shekara 18 da ya yi riga-kafin, sai dai akwai rukunin wasu mutane da aka ɗauke wa yin riga-kafin.
Sun haɗa da mata masu ciki da waɗanda suka yi riga-kafin korona a watanni shida da suka gabata da kuma waɗanda likitoci suka sahale musu yin riga-kafi saboda wasu larurori.
Wannan doka na nufin waɗanda ba a yi wa riga-kafi ba akwai yiwuwar su biya tara da ta kai dala 700.
Hukumomi sun bayyana cewa za a soma bincikar waɗanda ba su yi riga-kafin ba a watan Maris haka kuma za a ɗage tarar ga wadanda suka yi riga-kafin a cikin makoni biyu.