Connect with us

News

Duk da ya cika ƙa’idojin beli, har yanzu Ɗan-Sarauniya bai shaƙi iskar ƴanci ba

Published

on

FB IMG 16443061490044107
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

 

Advertisement

Har yanzu Muaz Magaji, babban ɗan adawar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, bai shaƙi iskar ƴanci ba duk da kotu ta bada belin sa a Ranar Juma’a, 4 ga watan Febrairu.

Kotun Majistare mai lamba 58, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Gabari ce ta bada belin Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan-Sarauniya, bayan ta aike da shi gidan yarin a ranar 31 ga watan Janairu.

Kotun na tuhumar Magaji, wanda fitaccen ɗan adawar Gwamna Ganduje ne da laifuka huɗu.

Advertisement

Laifukan sun haɗa da ɓata suna, cin mutunci da gangan, ƙarya da nufin zubar da kima da kuma ta da hankali, laifukan da su ka saɓa da sashe na 392, 399 da 114 na kundin dokar Kano ta 1999, amma kuma ya musanta duka laifukan.

Ƙa’idojin belin da kotun ta bayar sun haɗa da naira miliyan 1 da kuma waɗanda za su tsaya masa mutum biyu.

A cikin mutum biyun da za su tsaya masa, in ji alƙalin, a kwai Dagacin ƙauyen Ɗan-Sarauniya, sai kuma Kwamnadan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ko kuma Babban Limamin Ƙaramar Hukumar.

Advertisement

Hakazalika kotun ta bukaci Magaji da ya kai mata fasfo ɗin shi na tafiye-tafiye, inda su ma mutum biyun da za su tsaya masa sai sun kai hotunan su.

Sannan kotun za ta tura ma’aikatan ta su duba gidajen mutum biyun da za su tsayawa Magaji.

Sai dai Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa duk da ya cika waɗannan ƙa’idojin belin, har yanzu Magaji bai samu fitowa da ga gidan yari ba sakamakon Alƙali Gabari bai zauna ba a jiya Litinin.

Advertisement

Wasa-wasa dai Ɗan-Sarauniya ya kwashe kwanaki takwas a gidan yari.

Da yanke zantawa da Gidan Rediyon Freedom a Kano, lauyan Magaji, Ghazzali Ahmad, ya ce rashin zaman alƙalin ne ya sanya wanda ya ke karewa ya ƙara kwana ɗaya a gidan kaso.

Ya ce su basu san dalilin da ya sanya alƙalin bai zauna ba, inda ya ƙara da cewa duk wayar da su ka yi masa bai samu damar ɗagawa ba.

Advertisement

“Mun kikkira wayarsa, ba ya ɗagawa. Mu fatan mu, Allah Ya sa dai lafiya. Amma mu na sa ran alƙalin zai zauna yau kuma yanda hannu a sako wanda mu ke karewa,” in ji Ahmad.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *