Connect with us

News

Motoci na lalacewa bayan da NNPC ta shigo da lita miliyan 100 na gurɓataccen man fetur

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

 

Advertisement

Masu ababan hawa sun yi ƙorafin cewa injinan su sun lalace, musamman a Legas da Abuja sakamakon amfani da wani gurbataccen man fetur.

Lamarin na zuwa ne bayan da tuni layin man fetur ya dawo a gidajen mai a Abuja da Legas.

Wani ɗan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Daily Nigerian Hausa cewa NNPC ne ya yi odar man fetur ɗin da ke ɗauke da sinadarin sulphur da ya wuce kima.

Advertisement

Ya ƙara da cewa tuni ma yanzu haka akwai lita miliyan 100 na man da a ka rarraba a gidajen mai a faɗin ƙasar nan.

Da ga cikin gidajen man da a ka gano sun samu man akwai Total, Ardova, Enyo, Pinnacle, da sauransu.

Wasu majiyoyi sun ce tuni a ka faɗa halin siyan man na gudun ko-ta-kwana a wasu gidajen man yayin da kuma NNPC ke ƙoƙarin janye gurbataccen man.

Advertisement

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda wani mainsiyan mai ke ƙorafin yadda gurbataccen man ke lalata injina a gidajen mai.

Yayin da ya ke nuna wasu motoci da su ka buga, ya ce da yawa masu motocin sun kai korafi wajen yan sanda.

Ba a samu jin ta bakin Kakakin NNPC, Garba-Deen Mohammed ba har lokacin haɗa wannan rahoto.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *