Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya girmma wasu ƙwararrun ‘yan ƙasar uku da lambar yabo ta Nigerian National Order of Merit (NNOM) ta shekarun 2020 da 2021 ranar Talata.
Mutanen sun yi fice ne a ɓangarorin ilimi da suka haɗa da kimiyya da fasaha, da kuma likitanci.
Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, ya fitar ta ce Shugaba Buhari ya ce makomar Najeriya ta dogara ne kan yunƙurin ƙasar na shiga harkokin kimiyya da fasaha.
Ƙwararrun su ne: Dr. Oluyinka Olurotimi Olutoye, ƙwararre a likitanci (2020), da marigayi Farfesa Charles Ejike Chidume, kimiyya (2020), da Farfesa Godwin O. Samuel Ekhaguere, kimiyya (2021).
“Ina roƙonku da ku yi hoɓɓasa a kodayaushe don ƙarfafa gwiwar matasan Najeriya kuma ku tuna musu cewa makomarmu a matsayin ƙasa ta dogara ne kan shiga a dama da mu a cigaban duniya, musamman a ɓangaren kimiyya da fasaha,” kamar yadda shugaban ya faɗa wa mutanen.
Bai wa mutum ukun wannan lambar girma ta sa jumillar mutanen da suka same ta sun zama 79 tun bayan fara bayar da ita shekara 43 da suka gabata, a cewar Shugaba Buhari.