Shugaban hukumar yaki da masu sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (murabus) ya bukaci jami’o’in kasar da su bullo da tsarin yi wa dalibai gwajin miyagun kwayoyi domin raba matasa da ta’adar.
Ya nemi jami’o’in na Najeriya da su sa tsarin gwajin amfani da miyagun kewayoyin a kan sabbi da kuma daliban da ke karatu a cikinsu ya zama cikin manufofinsu.
Janar Marwa wanda ya bukaci hakan a yayin kaddamar da kamfe na yaki da miyagun kwayoyi a jami’o’i, Larabar nan 09 ga watan Fabrairu, 2022, a bikin da aka yi a Jami’ar Abuja, ya kuma nemi hadin kansu domin kafa kananan ofisoshin hukumar a makarantu domin taimaka musu a yaki da miyagun kwayoyi.
Marwa ya ce bullo da tsarin gwajin kwayoyin a kan dalibai ba yana nufin wani mataki na hukunta su ba ne, illa dai kawai ya zama wata hanya ta gano masu amfani da kwayoyin da wuri domin dakile matsalar tun daga tushe da yi musu magani.
Shugaban na NDLEA ya ce babu wani lokaci da ya wuce yanzu da ya kamata a tashi tsaye domin maganin matsalar ta amfani da miyagun kwayoyi saboda ta’ada ce da ta zama abar damuwa a