Entertainment
KA FARA YIWA YAYAN KA WAAZI KAFIN KA FITO KANA SURUTAI; Nuhu Abdullahi
Daga
Kabiru basiru fulatan
Hirar da kafar Bbc tayi da ɗaya daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood Ladi Cima, hirar ta jawo cecekuce a tsakanin al’umma da kuma manyan Jaruman Kannywood har ta saka an fara mayar da martani ta kakkausar murya.
Mawaki Naziru ya yi fashin baki sosai a kan haka kuma da alama ya goyi bayan hirar Ladin Cima kan rashin biyan hakkin aiki da tsoka a tsakanin Jarumai.
A saboda haka ne Jarumi Nuhu Abdullahi, yayi nashi maganganun inda yake sukar Naziru da cewar ya fara yiwa Yayan sa Aminu Saira waazi game da biyan hakkin kudin maaikata kafin yazo ya ce wani abu.
Har yake kn hankalin Naziru da cewar ya dena yiwa masu daukar nauyin shirin kudin goro.
Bayanin Jarumi Nuhu Abdullahi ya saka al’umma da dama suka koma baya kan ko rashin biyan hakkin aiki nada nasaba da dalilin dena fitowar Nuhu Abdullahi a cikin shirin Labarina?