Connect with us

News

Jiragen yaƙin Nijeriya, Super Tucanos sun hallaka ƴan ISWAP 34 a Marte

Published

on

FB IMG 1645089559109
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

A ƙalla ƴan ƙungiyar ta’addaci ta ISWAP 34 ne a ka kashe a garin Marte na jihar Borno a wani harin bamabamai da sojojin Najeriya suka kai ta sama, inji rahoton jaridar PRNigeria.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji tara na Rundunar Sojojin Kasa su ka samu munanan raunuka lokacin da ayarin motocinsu su ka yi taho-mu-gama da wasu nakiyoyi da ‘yan ta’adda su ka binne a garin Malam Fatori da ke karkashin karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

An ce sojojin na shirin kai hari ne kan wasu mayakan ISWAP da ke taruwa a Tumbun Dan Katsina.

Advertisement

Haka kuma, an samu rahoton cewa Rundunar Sojin Saman Najeriya, NAF, dakaru tare da dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa, MNJTF, a ranar Laraba, sun aiwatar da wasu hare-hare ta sama a sansanonin kungiyar ISWAP, a ranar Laraba a Sabon Tumbu, wani yanki mai fadama a karamar hukumar Marte da ke Jihar Borno.

Wata majiyar sirri ta ce harin na haɗin gwiwa da dakarun soji suka kaddamar ya biyo bayan wani rahoto ne da ke nuni da cewa an ga ‘yan ta’addar ISWAP sama da 100 a cikin kwale-kwale masu amfani da inji a Sabon Tumbu.

Majiyar, yayin da take zantawa da PRNigeria, ta tabbatar da cewa, jiragen Super Tucano da aka tura cikin gaggawa domin gudanar da aikin, sun kai farmaki maboyar ƴan ta’addar, inda su ka kashe da dama daga cikinsu.

Advertisement

Ya ce harin da a ka gudanar a yankin gaba daya ya nuna cewa an hangi ƴan ta’addar sun bushe a waje guda domin tsere wa daga harin da sojoji suka kai,” in ji shi.

Ya kara da cewa ci gaba da kai hare-hare ta sama ya yi tasiri a kan yaƙi da rundunar mayakan jihadi, tare da daƙile shirinsu na kai wasu manyan hare-hare a sansanonin soji a kewayen Malam Fatori, Damasak, Gubio da Kauwa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *