News
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta jingine hukuncin babbar Kotun tarayya kan rikin APC a Kano.

Daga yasir sani abdullahi
A baya dai Kotun tarayyar ta yanke hukuncin rushe zaɓen mazaɓu da ƙananan hukumomi na ɓangaren Gwamna Ganduje.
Sai dai a zaman Kotun ɗaukaka ƙara yau Alhamis a Abuja ta jingine wancan hukuncin bisa dalilin cewa kotun baya bata da hurumi.
Kotun ta kuma ƙara da cewa, rikici ne na cikin gida da uwar jam’iyyar ta ƙasa ke da alhakin daidaitawa.