News
An ja hankalin dalibai da su mayar da hankali kan karantun addini

Daga Abdulkadir Muhammad Sani
An ja hankalin dalibai da su mayar da hankali kan karantun addinin musulunci don tabbatar da samun ilimin zamantakewa mai cike da nagarta a rayuwa.
Babban malamin addinin musuluncin nan a yankin Tukuntawa, Sheikh Muhammad Sani Minsahawiy ne ya yi wannan jan hankali a wajen saukar karatun Al-Qur’ani karo na 4 na dalibai 17 maza da mata na makarantar .
Mu’assasatu Darul Islam Litahfizul Qur’an dake Tukuntawa.
Sheikh Minshawiy ya ce duk wanda yake karanta littafin ubangiji kuma ya haddace shi, to zai cece shi ranara gobe kiyama, sannan kuma ubangiji ya daga darajarsa.
Mutane dadama daga sassan yankin da dama ne suka halarci bikin saukar
da suka hada da Mai Unguwar Tukuntawa Malam Nuhu Garba.