Connect with us

News

Burtaniyya: Sarauniyar Ingila Ta Kamu Da Cutar Korona.

Published

on

FB IMG 1645441137947
Spread the love

Daga musa abubakar

 

.

Advertisement

Rahotanni daga Fadar Buckingham da ke Birtaniya, sun tabbatar da cewa Sarauniyar Ingila, Elizabeth II ta kamu da cutar Coronavirus, a yanzu dai Sarauniyar Ingila ita ce mutum ta baya bayan nan daga cikin mashahuran shugabannin duniya da cutar ta harba.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta hadu da babban danta kuma magajinta, Yarima Charles wanda ya sake kamuwa da cutar karo na biyu a makon jiya.

Fadar Buckingham ta bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa.

Advertisement

“Za a ci gaba da duba lafiyarta kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace,” kamar yadda fadar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.

Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan da sarauniyar ta kafa tarihi ta zama wadda ta fi dadewa kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ingila bayan ta cika shekara 70 a kan mulki a ranar 6 ga watan Fabrairu.

BBC ya ruwaito cewa babu shakka sarauniya an yi mata riga-kafin coronavirus zagaye na farko da na biyu.

Advertisement

Bayanai sun ce Sarauniyar tana bin rayuwa a hankali a ’yan kwanakin nan tun da ta kwana a asibiti a Oktobar bara yayin da ta  je duba lafiyarta.

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *