News
Amurka ta ƙaƙaba wa Russia sabbin takunkumai

Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Amurka, Joe Biden a ranar Alhamis ya sanar da ƙaƙaba wa Russia sabbin takunkumai bayan mamayewar da ta yi wa Ukraine, yana mai cewa shugaban ƙasar Vladimir Putin “ya zaɓi wannan yaƙi” kuma ƙasarsa za ta gaya wa aya zaƙinta.
Takunkumin ya shafi bankunan Russia, attajirai da ɓangaren manyan fasahohin zamani, in ji Biden.
Amurka da ƙawayenta za su toshe kadarorin wasu manyan bankunan ƙasar Russia guda huɗu, da sanya takunkumin hana fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da kuma sanya takunkumin karya tattalin arziki.
A ranar Talata ne Biden ya ba da sanarwar ƙaƙaba wa Russia kaso na farko na takunkumi, biyo bayan shawarar da ta yanke na amince wa da ƴancin kai na wasu yankunan Donetsk da Luhansk na Ukraine.
Shugaban ya sanar da takunkumin ne a fadar White House yayin da gwamnatin Ukraine ta bayar da rahoton karuwar asarar rayuka da sojojin Russia ke kaiwa da ga gabashi, arewaci da kuma kudu.
“Matakin takunkumin na sanya tsada mai tsanani kan manyan cibiyoyin hada-hadar kudi na Rasha kuma za su kara ware Rasha daga tsarin hada-hadar kudi na duniya.
Shugaban ya kuma gana da tawagar tsaron kasarsa a dakin taro na Fadar White House yayin da yake duba yiwuwar kawar da yunkurin Amurka a rikicin da ke kara kamari.