News
Russia kashe mana mutane 137 da kuma raunata 316, in ji Shugaban Ƙasar Ukraine

Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelesnky ya yi koken cewa an hallaka a ƙalla mutane 137, har da fararen hula a hare-haren da Russia ke kai wa ƙasar.
Zelesnky ya kuma ƙara da cewa hare-haren ya yi sanadiyar raunata mutane 316 a ƙasar.
Shugaban Ukraine din na ganin shi ne mutum na farko da Russia ke hari, inda ya ci alwashin cewa ba shi da niyyar barin gidan gwamnatin da yake zaune a birnin Kyiv.
Ya kuma tabbatar da rahotannin da ke cewa Russia ta harba makamai masu linzami masu yawa a cikin Ukraine da misalin ƙarfe huɗu na asuba agogon ƙasar.
Ya kƙara da kira ga ƙasashen yamma da su ƙara ƙoƙari kan saka takunkumai ga Russia, inda ya buƙaci su yi abin da ya fi saka takunkumin tattalin arziki ga ƙasar.
A wani gargaɗi da ya yi ga Moscow, Zelensky ya bayyana cewa Ukraine ba za ta daina kare kanta ba har sai Russia ta daina abin da take yi.