Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mbappe, Haaland, Bielsa, Nunez, Diaz, Botman, Christensen, Isak
Daga kabiru basiru fulatan
Real Madrid na da yaƙinin tana da kuɗaɗen da ake bukata na cimma yarjejeniya da ɗan wasan Paris St-Germain da Faransa mai shekara 23, Kylian Mbappe, da kuma ɗan wasan gaba a Borussia Dortmund dan asalin ƙasar Norway Erling Braut Haaland ɗan shekara 21 a wannan kakar. (Marca)
Kocin Leeds United Marcelo Bielsa na gabar fuskantar kora daga ƙungiyar, tsohon kocin RB Leipzig Jesse Marsch ya kasance wanda ake tunanin maye gurbinsa da shi. (Mail)
Liverpool na son dauko ɗan wasan Benfica da ke buga gaba Darwin Nunez mai shekara 22, yayinda ɗan wasan asalin Uruguay ya matsu ya koma Reds. (Football Insider)
Kocin West Ham David Moyes ya ce ya tattaunawa ɗan wasan Colombia mai buga gaba Luis Diaz a kokarin saye shi kafin Liverpool ta dauke shi.(Football London)
Daya daga cikin masu Newcastle United Amanda Staveley na cewa ɗan wasan Lille mai shekara22 Sven Botman da kuma Manchester United Jesse Lingard mai shekara 29, duk sun so komawa ƙungiyar a watan Janairu. (Athletic – subscription required)
Tottenham na fatan doke Newcastle a cinikin saye Botman domin nunawa Antonio Conte cewa ƙungiyar ta dawo da karfinta. (Star)
Barcelona da Bayern Munich na fafatawa a kokarin kulla ciniki da ɗan wasan Chelsea Andreas iChristensen. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Ɗan wasanReal Sociedad da Sweden Alexander Isak mai shekara 22 na bada fifiko kan komawa Barcelonamaimakon Arsenal a karshen kaka. (Sport via Metro)
Manchester United na sanya ido kan ɗan wasan PSV Eindhoven da Netherlands Cody Gakpo da ɗan wasan Sporting Lisbon da Portugal Joao Palhinha. (Mirror)
Barcelona na shirya gabatar da tayi kan ɗan wasan Manchester United Eric Bailly mai shekara 27 asalin Ivory Coast. (Star)
Tsohon mai buga tsakiya a Arsenal Paul Merson ya shaidawa kulob din cewa ta sayar da Bukayo Saka ɗan shekara 20 da mai buga tsakiya Emile Smith Rowe mai shekara 21. (Star via Mirror)
Ɗan wasan Ingila Ashley Fletcher mai shekara 26 daya koma Watford a kakar da ta gabata na shirin tafiya aro Red Bulls da ke New York (Watford Observer)
Max Kilman na Wolves na kwokwanton ko kocin Ingila Gareth Southgate zai gayyace su wasannin sada zumunta a watan Maris. (Mirror)