Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki bayar da belin Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar.
A ranar 14 ga Fabrairu, rundunar ƴan sanda ta miƙa Abba Kyari ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) da ayyana tana nemansa ruwa a jallo kan badaƙalar safarar hodar iblis kilo 25.
Kyari ne ya shigar da kara yana ƙalubalantar gwamnatin tarayya kan keta haƙƙinsa tare da bayyana safarar miyagun kwayoyi da ake yi masa a matsayin ƙage.
Kyari ya nemi kotun tarayaya ta bayar da belinsa kan dalilai na rashin lafiya, inda lauyoyinsa suka ce yana fama da ciwon suga da hawan jini.
Kotun bayan watsi da buƙatar belin ta kuma ɗage sauraren ƙarar da Abba Kyari ya shigar kan keta haƙƙinsa zuwa 15 ga watan Maris