News
Yajin aikin ASUU: Mun biya malaman jami’o’i Naira Biliyan N92.7bn –Ngige

Daga muslim yunus Abdullahi
Ministan Ƙwadago da samar da Ayyukan yi, Chris Ngige ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari karin haske kan tattaunawar da a ke yi tsakanin Gwamnatin Taraiya da ƙungiyar malaman jami’o’i.
A tuna cewa ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na tsawon wata guda tun ranar 14 ga watan Fabrairu sabo da gazawar gwamnati wajen cimma yarjejeniyoyin da aka yi da ita.
Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron, ministan ya ce shugaban ƙasar ya gamsu da bayanin da ya yi masa.
Ya ce: “Za mu aiwatar da yarjejeniyar 2020 da a ka yi da ASUU,”
A cewar sa, gwamnatin tarayya ta biya Naira biliyan 40 na alawus-alawus da kuma Naira biliyan 30 domin walwalar malaman.
Ya kara da cewa an kuma biya Naira biliyan 22.7 da ga ƙarin kasafin kuɗi sannan a ka ba su alawus-alawus na 2021.