Connect with us

News

Ƴan Najeriya na ce-ce-ku-ce kan bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai

Published

on

1646240560294

Daga Usman Abdullahi jibirin

Wasu ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta sun nuna ɓacin ransu bayan ganin wani bidiyo da ya nuna yadda wasu matan gwamnonin jihohin ƙasar na taya uwar gidan shugaba Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarta a ƙasar Dubai.

Advertisement

A ranar 17 ga watan Fabrairu ne Aisha Buhari ta yi bikin cika shekaru 51 a duniya, amma sai yanzu bidiyon ya fito. Babu tabbaci kan lokacin da aka ɗauki bidiyon.

Bidiyon ya nuna wasu gungun mata da kafafen yaɗa labaran Najeria suka ce matan ƴan siyasar ƙasar ne ɗauke da wani ƙaton akwati da furanni, suna rera waƙar murnar zagayowar ranar haihuwa ga Aisha Buhari. Akwai kuma mai daukar hoto a baya.

Advertisement

Wasu sun bayyana mamakin yadda waɗanda suka halarci bikin suka kashe kuɗin jirgi zuwa Dubai.

“Nawa ne daga cikinsu za su yi amfani da kuɗin aljihunsu,” kamar yadda wani mai amfani da Twitter ya bayyana.

Advertisement

Wasu kuma na ganin matan ƴan siyasar sun kama hanya sun tafi biki a daidai lokacin da ƙasa ke fuskantar tarin matsaloli.

“Wannan rashin hankali ne sosai kuma abin baƙin ciki ne”, kamar yaddawani ya rubuta.

Advertisement

Bidiyon bai nuna ko shugaba Buhari yana wajen bikin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending