Sports
Ƴan ƙwallon ƙafar Ukraine 2 sun mutu a wajen yaƙi da Russia
Khadija Abdullahi Muhammad
Kungiyar ‘yan wasan ƴan ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFPRO ta tabbatar da cewa an kashe ƴan wasan ƙasar Ukraine biyu a yaƙin da suke yi da Russia.
Vitalii Sapylo mai shekaru 21 da Dmytro Martynenko mai shekaru 25 sun mutu a yaƙin, bayan da sojojin Russia su ka mamaye Ukraine bisa umarnin shugaba Vladimir Putin.
Sapylo ya kasance mai tsaron raga tare da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Karpaty Lviv mai buga hada ta rukuni na uku, yayin da Martynenko ya ke buga wa kungiyar FC Hostomel ta rukuni na biyu.
Sanarwar da FIFPRO ta fitar a shafinta na Twitter ta ce: “Mu na ta’aziya ga iyalai, abokai, da abokan wasan matasa ‘yan wasan kwallon kafa na Ukraine Vitalii Sapylo da Dmytro Martynenko, su ne na farko da aka bayar da rahoton mutuwar su a wannan yakin. Ubangiji Ya jikan su.”