Connect with us

News

NDLEA ta gabatar da tuhuma takwas ga DCP Abba Kyari da wasu mutum shida

Published

on

1646379287768
Spread the love

 Daga Usman Abdullahi Jibirin

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gabatar da tuhuma takwas ga DCP Abba Kyari da karin mutum shida, a gaban wata babbar kotun tarayya ta Abuja bisa zargin hannunsu da fataucin kwayoyi.

Wannan na zuwa ne ‘yan sa’o’I da hukumomin kasar suka amince su mika ɗan sanda Abba Kyari hannun Amurka.

Advertisement

NDLEA ta gabatar da tuhume-tuhumen ne a gaban kootun tarayya da ke Abuja a kan ACP Sunday Ogbuya da ACP Sunday James da Sifeta Simon Ariba da kuma Sifeta John Nuhu, wadanda suka yi aiki da runduna ta musamman da ke yaki da iyagun laifuka ta Police Intelligence Response Team.

Da kuma wasu mutum biyum Chibunna Patrcike da Emeka Alfphosus, wadanda aka kama su a filin jirgin sama na Enugu bisa zarginsu da laifuka da suka shafi batun muggan kwayoyi ciki har da hodar ibilis.

Rahotanni sunce tawagar lauyoyin NDLEA karkashin jagorancin Mr Joseph Sunday ta shigar da kara inda ta zargi DCP Abba Kyari da sauran jami’an ‘yan sanda hudu da hada baki wajen safarar hodar ibilis mai nauyin fiye da kilogiram 17.

Advertisement

Kazalika an yi zargin cewa Abba Kyari da mutanenssa da ke tsare a yanzu a hannun NDLEA sun jirkita kunshin hodar ibilis da ya kai nauyin kilogiram 21.

Hakan na zuwa ne a yayin da ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana amincewa da bukatar Amurka ta mika mata DCP Abba Kyari bisa zarginsa da hannu wajen aikata zambar fiye da dala miliyan daya ta intanet tare da Hushpuppi.

Ana sa ran a gobe ne za a saka ranar da za a fara sauraron karar da NDLEA ta shigar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *