News
Ƴar shekara 16 ta rasu a rijiya a Kano
Daga kabiru basiru fulatan
Wata yarinya ƴar shekara 16, Hamida Bawale ta rasu bayan ta faɗa rijiya a Kofar Fada Gidan Sarki a Ƙaramar Hukumar Karaye da ke Jihar Kano a jiya Talata.
Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta Kano, Saminu Abdullahi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiyan.
Ya ce lamarin ya faru da yammacin jiya Talata, bayan da Hukumar ta karbi kiran gaggawa da ga ofishin Hukumar Kare Farar-hula, NSCDC, reshen Karaye da misalin ƙarfe 4:58.
A cewar Abdullahi, da ga karɓar rahoton, sai hukumar ta yi maza ta tura jami’an ta na ɓangaren bada agaji, inda su ka isa wajen da misalin ƙarfe 5:04 na yamma.
Da zuwan su, inji Abdullahi, sai su ka ɗauko Hamida, amma tuni rai ya yi halin sa, inda su ka miƙa gawar ta ta zuwa ga yayanta, Abdullahi Bawale.
Kakin ya ƙara da cewa marigayiyar ta gamu da ajalin ta ne bayan da ta je debo ruwa a rijiyar shine ta faɗa ciki.
Sai dai kuma sanarwar ta ce Hamida na fama da ɗan taɓin hankali.