News
Kotu ta aike da Ɗan-Bilki Kwamanda zuwa gidan yari bisa zargin ɓata suna ga Ganduje

Daga abbas sani abbas
A jiya Talata ne dai a ka gurfanar da Abdulmajid Ɗan-Bilki Kwamanda, ɗan siyasa kuma babban masoyin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Kano, a gaban kotun majistire mai lamba 58 ƙarƙashin mai Shari’a Aminu Gabari.
Kotun dai na tuhumar Kwamanda da zargin laifiuka 3, da su ka haɗa da ɓata suna, kalaman ɓatanci da yunkurin ta da hankali, laifukwn da su ka saɓa sashe na 392 da 393 na dokar ‘Penal Code’ ta Kano.
Da a ke karanto wa Kwamanda laifukan sa, cewa a wata hira da ya yi a gidan rediyo, ya zargi Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da baiwa Shugaban Riƙo na APC na Ƙasa, Mai Mala Buni cin hanci, shi ya sa a ka baiwa Abdullahi Abbas shaidar zama cikakken Shugaban Jam’iyya na Jihar Kano, sai ya nisanta zargin.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kwamanda ya faɗi zargin ne bayan da wani hadisin mataimakin shugaban kasa, Alwan Hassan, a wani fefen bidiyo da ya ke ta yawo, ya yi zargin cewa Ganduje ya baiwa Buni cin hancin.
Da ga nan ne sai lauyan gwamnati, Barista Wada A. Wada ya shaida wa kotu cewa tun da wanda a ke zargi ya musanta zargin, su na roƙon a basu wata rana domin kawo shaidunsu a gaban kotun.
Ya kuma yi rokon da a umarci ƴan sanda su kawo kundin bayaninsu na bincike akan wanda a ke ƙara.
A nashi ɓangaren, lauyan kwamanda, Barr. Ibrahim Chedi, ya yi rokon da a sanya wanda ya ke kare wa a hannun belli, inda ya bada tabbacin cewa za su tabbatar da cika dukkanin wasu ka’idojin da kotu ta gindaya.
Da ga nan ne sai Mai shari’a Aminu Gabari ya yi umarni ga mai gabatar da ƙara da ya kawo wa kotu shaidu.
Sannan ya yi umarni da a ajiye Kwamanda a gidan gyaran hali har sai zuwa ranar 15 watan Maris.