Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Haaland, Silva, Tuchel, Tielemans, Messi, Tchouameni

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Real Madrid ta fara yanke kauna a fatan da take na doke Manchester City wajen sayen tauraron dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland. (Goal)

Advertisement

Dan wasan Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 27, ya ce yana fatan komawa kasarsa da wasa inda zai je kungiyar Benfica a shekara biyu nan gaba. (Mail)

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa zai tafi Manchester United, yana mai cewa kungiyarsa ta Stamford Bridge tana da duk wani abu da yake bukata da za ta sa shi farin ciki. (Metro)

Advertisement

Ana sa ran Manchester City ta tsawaita kwantiragin dan wasanta na tsakiya na Sifaniya Rodri, wanda kwantirginsa na yanzu zai kare a 2025. (Telegraph – subscription required)

Dan wasan Belgium Youri Tielemans, wanda kwantiraginsa da Leicester City zai kare a 2023, ya ce tattaunawa na gudana da kungiyar tasa a game da zamansa a kungiyar, kuma dan wasan ya ce zai yi nazari a kan zabin da yake da shi a bazaran nan. (Metro)

Advertisement

Dan bayan Brazil Dani Alves, mai shekara 38, ya ce Lionel Messi ba ya jin dadin zamansa a Paris St-Germain kuma yana fatan Messin zai iya dawowa Barcelona. (Mirror)

Dani Alves

Manchester United da Inter Milan sun sa ido a kan dan bayan Fiorentina dan Serbia Nikola Milenkovic, mai shekara 24. (Football Italia)

Real Madrid na sha’awar dan wasan tsakiya na Monaco Aurelien Tchouameni to amma kuma dan wasan na Faransa yana sha’awar tafiya Ingila ne inda Liverpool da Manchester City da kuma Manchester United ke sonsa. (Marca)

Advertisement

Ba a sanya golan Manchester United David de Gea, a cikin tawagar Sifaniya da za ta kara a wasan sada zumunta da Albania da Iceland ba, saboda bai dace da tsarin wasan tawagar ba. (Manchester Evening News)

David de Gea

Manchester City ta amince ta sayi matashin dan wasan gaba na kungiyar Atletico Mineiro Savio, mai shekara 17, wanda ya yi wa tawagar Brazil ta matasa wasa, a kan fam miliyan 5.4. (Goal)

West Ham ta bi sahun Newcastle United wajen sanya ido a kan dan wasan tsakiya na Faransa Ludovic Blas, mai shekara 24, wanda ke kungiyar Nantes. (Football Transfers)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending