Connect with us

Sports

Italiya ba za ta je gasar kofin duniya ba.

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

Tawagar ‘yan wasan kasar Italiya ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Macedonia del Norte, a daren ranar Alhamis wanda hakan ya sa ba za ta samu tikitin zuwa gasar kofin duniya da za a gudanar a kasar Qatar ba.

Wannnan shi ne karo na biyu ra kasar ke gaza zuwa gasar kofin duniya a jere.

Advertisement

Roberto Mancini ya yi rashin nasara mafi radadi a rayuwarsa ta harkar horarwa, bayan a daren Alhamis.

Mancini dai ya zama gwarzo, inda kimarsa ta karu a idon duniya da kasarsa Italiya, bayan da ya jagoranci tawagar kwallon kafar kasar daga yanayin rashin katabus na gaza shiga gasar turai, zuwa lashe kofin gasar Euro 2020 a bara.

Sai dai tun daga wannan lokacin tawagar kwallon kafar Italiya ta fara fuskantar matsalar rashin tabuka wani abu.

Mancini ya shaida wa manema labarai cewa, kamar yadda watan Yuli shekarar da ta gabata ya kasance cikin yanayi mafi armashi a sana’arsa ta horar da kwallon kafa, haka ma wannan wata na Maris ya kasance masa mafi muni.

Mancini bai yi wani bayani a game da ci gaba da aiki da tawagar Italiya ba, amma shugaban hukumar kwallon kafar kasar Gabriele Gravina, ya ce yana so Mancini ya ci gaba da jagorancin tawagar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending